Barka da zuwa shafin Koyo tare da KT

Koyi yadda akeyi, kayi noma mai ban mamaki!


Koyi dabarun noman lambu daga kwasakwasan dake kan intanet kyauta har da shaidar kammalawa. Kwararru daga East West Seed Sashen yada Ilimi da Jami'ar Wageningen da kuma gidauniyar Koppert ne suka shirya kwasakwasan.


Yi duba akan kwasa-kwasan mu


Noman Lambu ga wanda ya fara

Noman Lambu ga wanda ya fara shiri ne da aka tsara shi don wadanda suke da sha'awar samun ilimi na fasaha akan noman kayan lambu.


Mai bada shawara akan noma

Kwas din mai bada shawara akan noma an shirya shi ne don masu horo na musamman akan fasaha na East West Seed da sauran abokan hulda wanda suke so su samu ilimin fasaha a noman lambu.


Kasuwancin noma

Kwas din kasuwancin noma an shirya shi ne don masu siyarda kayan nomadon su samu damar bada shawarwari ga kwastamominsu akan dabarun noman lambu.


Tambayoyin da aka fi tambaya


  • Mecece East West Seed Sashen yada ilimi?
    EWS-KT gidauniya ce wanda aka kafa ta ba don samun riba ba kuma wanda ta ke da alaka da Kamfanin East-West Seed. Aikinmu shine inganta rayuwar manoma masu kananan karfi a wuraren da basu bunkasa sosai ba na Afurka da Asiya. Ta hanyar samar da damammaki don inganta kudin shiga, aikinmu na kara habaka samuwar kasuwannin kayan noma da kuma kara samuwar kayan lambu masu inganci da araha a kasuwanni wanda ke kai wa ga kwastamomi masu kananan karfi.

  • Me ake nufi da koyo tare da KT?
    Koyo tare da KT wani dandali ne na yanar gizo wanda East West Seed Sashen Yada Ilimi tare da TalentLMS suka shirya shi don samar da wani dandali na karatu ga masu son koyan noman lambu. Koyo tare da KT na da burin samar da kwarewa ta hanyar cakuda darussan koyo ta yanar gizo tare da ziyara zuwa gonaki duka ta yanar gizo, kafafe, shawarwari da sauransu don masu son koyo ko kuma kwararru a noman lambu.

  • Wa ya tsara wadannan kwasa kwasai?
    Wannan kwas din EWS-KT Technical Support Hub ne suka shirya shi, ta hanyar bin diddigin iliminsu wanda East-West Seed na fiye da shekaru 40 tare da tallafawar Jami'ar Wageningen. An shirya kwas din ne don yayi daidai da bukatun mutane daban daban.
  • Shin ana biyan kudi don yin wadannan kwasa kwasan
    Kwasa kwasan kyauta ne. Ba a bukatar kudi don yin su ko kuma don shaidar kammalawa

  • Kwasakwasai guda nawa zan iya yin rajistarsu kyauta a lokaci daya?
    Kwas daya ake iya yin rajista a lokaci daya.
  • Ta yaya ake tantance ayyuka da kacici-kacicin da aka bayar?
    An riga an amsa tambayoyin wanda kai tsaye na'ura ke dubawa kai tsaye.
  • Ta yaya zan samu shaidar kammalawa?
    Idan ka kammala kwas din cikin nasara kuma ka samu maki 80%, za a baka shaidar kammalawa kai tsaye
  • Wadanne kwasa-kwasai aka fi bada su kyauta?
    A wannan lokacin, East West Seed sashen yada ilimi na bada kwasa-kwasai 3: Kwas din noman lambu ga wanda ya fara, Kwas din kasuwancin noma, Kwas din mai bada shawara akan noma
  • Waye ya cancanta da yayi wadannan kwasa-kwasai kyauta?
    Kwasa-kwasan a bude yake ga duk mai son koyan dabarun noman lambu wanda zai taimaka musu da manoma masu kananan karfi wajen inganta nomansu da kudaden shigarsu.l